za ayiwa yan takara gwajin kwaya a kano
Shugaban hukumar zaɓe na jihar Kano, pro Sani Lawal Malumfashi, yace sai an yiwa duk wani ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi gwajin ƙwayoyi kafin a bashi damar tsayawa takara.
pro sani lawan, ya fadi hakan ne a yayin wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a jihar Kano a ranar Alhamis.
A yayin taron, hukumar zaben ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen da za ayi to zai sayi fom a kan naira milian 10.
Yayin da ɗan takarar kansila kuma kuɗin fom ɗinsa ya zai biya naira miliyan 5.
Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar kano ne a ranar 30 ga watan Nubember 2024