yan bunduga sun kashe sarkin gober
Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji’un! Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir bayan wa’adin da suka sa na a kai masu kudin fansarsa na Naira miliyan ɗari biyar ya kare
Rahotannin da muke samu daga jihar Sokoto na cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun kashe shi.
A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kudin fansa da suka bukata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.
Mako uku da suka wuce ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da sarkin a yankin kwanar maharba lokacin da yake kan hanya bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.
A hirarsa da BBC, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin Gobir, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.
“Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya [Talata] bayan la’asar, kuma waɗanda suka je tattauna biyan kuɗin fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su samu gawar mai martaban ba tukunna.