kayan abunci akaran farko sun fara sauka a nigeria
Hukumar ƙididdiga ta kasar Najeriya ta sanar a ranar Alhamis cewa, hauhawar farashin kayayyaki abunci a ƙasar ta sun sauka a karon farko da kashi 33.4 cikin 100 a watan Yuli inda aka kwatanta da kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin shekarar da muke ciki 2024.
Kayayyakin da farashin nasu ya fara sauka sun haɗa da shinkafa da masara da ƙwai da burodi da man petrol.
To amma dai kuma farashin makamashi na ci gaba da tsada a cikin shekara ɗaya da ta wuce a cewar hukumar kididdigar.
Najeriya dai ta fara aiwatar da manufofin ta na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar tun a shekarar bara.
Ƙasar ta dauki matakai kamar cire tallafin man fetur da kuma farfado da darajar naira ƙasar.
Shugaba ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen na da matukar alfanu kuma ya zama dole da nufin farfaɗo da tattalin arziƙin kasa.
A farkon watan Augusta ne ƴan kasar suka gudanar da zanga-zanga a kan matsin rayuwa ta kwana 10 don matsawa gwamnati ɗaukar matakan sassauta al’amura da tsadar rayuwa.
allah yasa mudace kutubuta mana ra ayin ku a comment