nigeria,NAHCON,EFCC,arest

hukumar EFCC Ta kama shugaban NAHCON

Share it

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar nigeria  zagon ƙasa, EFCC ta ce shugaban Hukumar Alhazan Ƙasar nigeria  NAHCON, (Malam Jalal Arabi) yana hannunta inda take gudanar da bincike a kansa.

 

nigeria,NAHCON,EFCC,arest


 

Mai magana da yawun hukumar yaki da rashawa na kasa  EFCC Dele Oluwale ne ya tabbatar wa TRT Afrika hakan a wata gajeriyar zantawa ta wayar tarho a ranar Alhamis.

 

“Haka ne labarin da kuka ji, shugaban NAHCON na wajenmu tun ranar Talata inda muke gudanar da  binciken badakala a kansa,” in ji Mista Oluwale.

 

Amma mai magana da yawun EFCC ɗin ya ƙi yin wani ƙarin bayani a kan rahotan, yana mai cewa “ba zan ƙara komai a kan wannan ba saboda bincike muke yi har yanzu a kansa bamu tabbatar ba.”

Sai dai rahotanni da dama a faɗin ƙasar sun ce EFCC tana zargin Malam Arabi ne da almubazzaranci da rarar kuɗaɗen Aikin Hajjin 2024 da suka kai yawan Naira biliyan 90.

Wasu rahotannin sun ce tuni har EFCC ɗin ta ƙwato Riyal 314,098 na saudiyya  daga wajen shugaban na NAHCON da wasu manyan jami’an NAHCON hukumar da ake zarginsu tare.

KURUBUTAMANA RA AYIN KU A COMMENT SECTION

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *