HANKALIN MANYAN KASASHEN DUNIYA YA KARKATO ZUWA GA ZALUNCIN YAN SIYASA
HANKALIN MANYAN KASASHEN DUNIYA YA KARKATO ZUWA GA ZALUNCIN YAN SIYASAR NIGERIA, DA GOYAN BAYAN TALAKA.
Bayan ‘Gano’ Albashin Sanatocin Najeriya, ‘Dan Majalisar Amurka Ya Gargadi Tinubu.
Dan majalisar Amurka, Beroro Efekoro ya turo gargadi ga gwamnatin Najeriya bayan gano albashin ‘yan majalisar dattawa Beroro Efekoro ya ce yadda yan majalisar Najeriya ke diban kudi da sunan albashi da alawus ya wuke yadda hankali zai dauka.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne ya fara tono zance, ya ce ‘yan majalisar Najeriya ke yankewa kansu kudinsu.
Maganar albashi da alawus din yan majalisar dattawan Najeriya na cigaba da jan hankulan al’ummar duniya.
Wani dan majalisa a kasar Amurka, Beroro Efekoro ya nuna takaici kan yadda Sanatocin Najeriya ke samun kudi sosai da sunan albashi da alawus.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Beroro Efekoro ya bayyana lamarin ne a birnin New York da ke kasar Amurka.
Beroro: “‘Yan siyasar Najeriya suna cutar talaka”
The Nation ta wallafa cewa dan majalisar kasar Amurka, Beroro Efekoro ya ce gwamnatin Najeriya da yan siyasa suna suna son kai talaka bango.
Beroro Efekoro ya fadi haka ne kan yadda yan siyasa ke wadaka da dukiya alhali talakawa na fama da yunwa da talauci.
Kiran ‘dan majalisar ga gwamnatin Tinubu
Dan majalisar ya ce akwai bukatar gwamnatin Tinubu ta fito da manufofinta fili ta yadda za ta gamsar da yan kasa.
Ya kuma kara da cewa gamsar da yan kasa ne kawai zai hana juyin juya hali da alamunsa suka bayyana a Najeriya.
Beroro ya tura sako ga shugaban majalisa
Beroro Efekoro ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya nisanci yin barazana ga Sanatoci da suke sukar gwamnati.
Ya ce bai kamata a ce majalisar dattawa ta zama ‘yar amshin shatar gwamnatin tarayya ba matuÆ™ar ana son kawo cigaba.
Tun abaya an bukaci matasa su shirya tsarin kiranye (Recall) ga yan majalisu da sanatoci kafin 23 ga wannan watan. Ko kuma su gyra halin su akan halin da talaka ke ciki a Nigeria.
Kun fara shirin a yankin ku kuwa?