Gwamnatin jihar Enugu ta umarci churchi da masallatai da su jire lasifikokim su na waje
Gwamnatin jihar Enugu ta umarci churchi da masallatai da su jire lasifikokim su na waje
Gwamnatin jihar Enugu a Najeriya ta bada umarnin dukkanin churchis da masallatai a jihar dasu cire duk wata lasifika da suka sa a wajen gine-ginensu cikin kwanaki (90), kuma su dauki matakan tabbatar da cewa hayaniya ko karar abubuwan da ake yi a cikin wuraren ibadar ba ta fitowa waje majamiun ko masallacin.
An dauki matakin ne a yau Alhamis, a lokacin wani taro tsakanin hukumomin da shugabannin Kiristoci da Musulmi na jihar, kan aiwatar da tsarin gwamnatin jihar na takaita hayaniya a jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar raya babban birnin jihar ta Enugu, Uche Anya, wanda ya fada da umarnin ya ce hayaniya da kara sun zama babbar matsala ga jihar.
Shugaban ya nuna takaicin yadda offishin ya samu kararraki sama da dubu 1,000, daga masu gidaje a kusa da wasu coci-coci da masallatai da wuraren rawa joint joint ko shaye-shaye da makamantansu a kan kara ko hayaniya da ke cimusu tuwo a kwarya
A shekarar da ta wuce, 2023, gwamnatin jihar inugun, da ke kudu maso gabashin nigeria, a wani mataki na sake tsarin raya biranenta, ta umarci dukkanin wuraren nishadi da joint joint da shaye-shaye da kade-kade da sauran abubuwa na walwala da su rage hayaniyar da ake yi a wuraren, a babban birnin jihar, musamman ma a unguwannin da gidajen da jama’a suke.