A hukuman ce: Thiago Alcântara ya bar aikinsa na koci a Barcelona
Thiago Alcantara ya yi ritaya daga ball , bayan da contract dinsa ya kare a Liverpool.
Tsohon ɗan wasan tawagar spain, mai shekara 33 ya buga wasa ɗaya a kakar 2023-24 a ƙungiyar sa ta liverpool a Anfield, sakamakon jinya rauni.
Thiago wanda aka yi wa tiyata a kunkuru a 2022-23, bai warke ba sai cikin feb 2024, wanda ya koma wasa a karawa da kungiyar Arsenal,
inda ya kara jin ciwo a fafatawar sa.
Shi ne wasa na 98 da ya wakilci Liverpool tun bayan da ya koma ƙungiyar kan kaka hudu daga kungiyar Bayern Munich a 2020 wato yaya babba.
Thiago ya lashe FA Cup a Liverpool a 2021–22, wanda a baya ya bayar da gudunmuwar a Bayern munich ta ɗauki Bundesliga a kaka 7 da Champions League a 2019–20.
Ya fara buga leda a Barcelona da ɗaukar La Liga da Champions League ɗaya daga nan ya koma Bayern a 2013.
Wanda aka haifa a italy – mahaifinsa tsohon ɗan wasan tawagar Brazil, Mazinho ne a lokacin da yake murza leda a Lecce.
Thiago ya koma Barca a lokacin da yake da shekara 14 na haihuwa, ya wakilci spain, wadda ya buga wa karawa 46 tsakanin 2011 zuwa 2021.